A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Ayatullah Bahjat, yayin da yake bayani kan tasirin ruhi na faranta ran muminai, ya yi magana kan alaƙar da ke tsakanin wannan kyakkyawan aiki da falala da kariyar Allah. Ya kuma tunatar da cewa faranta ran ma'abota imani na iya zama sanadin kare mutum daga musibu da haɗurra.
Ayatullah Bahjat (Allah Ya jiƙansa) ya ce:
“Idan ka faranta ran wani mumini, Allah kan halicci wani mala'ika daga falalarsa, wanda wannan mala'ikan zai riƙa kare ka daga musibu, haɗurran mota da sauran abubuwa makamantansu."
Dalilin da ya sa kake ganin cewa a wasu haɗurran mota wasu mutane suna tsira, alhali kuwa wanda ke zaune kusa da su ya samu rauni, shi ne saboda wannan mutumin da ya tsira ya taɓa taka rawa wajen faranta ran ma'abota imani.
Manazarta: Littafin Baragi az Daftare Aftab, shafi na 184.
Ra'ayinka